2 Sam 10:10-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sauran mutane kuwa ya sa su a hannun Abishai, ƙanensa. Ya sa su gabza da Ammonawa.

11. Ya ce musu, “Idan Suriyawa sun fi ƙarfina, ku kawo mini gudunmawa, amma idan Ammonawa sun fi ƙarfinku, sai in kai muku gudunmawa.

12. Mu yi ƙarfin hali, mu yi jaruntaka saboda jama'armu da biranen Allahnmu. Ubangiji ya yi abin da ya gamshe shi.”

13. Sa'an nan Yowab da mutanensa suka matsa, su gabza da Suriyawa. Suriyawa kuwa suka gudu.

14. Da Ammonawa suka ga Suriyawa sun gudu, su ma suka gudu daga gaban Abishai suka shiga birnin. Sa'an nan Yowab ya komo Urushalima daga wurin yaƙi da Ammonawa.

15. Sa'ad da Suriyawa suka ga Isra'ilawa sun ci su, suka tattara kansu.

16. Hadadezer ya aika aka kawo Suriyawan da suke a hayin Kogin Yufiretis. Suka taru a Helam. Shobak shugaban rundunar Hadadezer shi ne ya shugabance su.

2 Sam 10