5. Daga cikin dukan 'ya'yana maza, (gama Ubangiji ya ba ni 'ya'ya maza da yawa), ya zaɓi ɗana Sulemanu ya hau gadon sarautar Isra'ila, abin mulkin Ubangiji.
6. “Ya ce mini, ‘Ɗanka Sulemanu ne zai gina Haikalina da shirayuna, gama na zaɓe shi ya zama ɗa a gare ni, ni kuwa in zama uba a gare shi.
7. Zan tabbatar da mulkinsa har abada idan ya bi umarnaina da ka'idodina da himma kamar yadda ake yi a yau.’
8. “Saboda haka a gaban dukan Isra'ila, wato taron jama'ar Ubangiji, da kuma gaban Allahnmu, sai ku kiyaye, ku bi dukan umarnan Ubangiji Allahnku don ku mallaki ƙasan nan mai kyau, ku kuma bar wa 'ya'yanku ita gādo har abada.
9. “Kai kuwa ɗana Sulemanu, sai ka san Allah na tsohonka, ka bauta masa da zuciya ɗaya, da kuma yardar rai, gama Ubangiji mai binciken dukan zukata ne, ya kuma san kowane irin nufi da tunani. Idan ka neme shi, za ka same shi, in kuwa ka rabu da shi, shi ma zai yi watsi da kai har abada.
10. Ka lura, gama Ubangiji ya zaɓe ka domin ka gina Haikali, wato Wuri Mai Tsarki. Ka yi ƙarfi, ka kama aiki.”
11. Sa'an nan Dawuda ya ba ɗansa Sulemanu tsarin shirayin Haikalin, da ɗakunansa, da ɗakunan ajiya, da benaye, da Wuri Mafi Tsarki, inda ake gafarta zunubi.
12. Ya kuma ba shi tsarin dukan abin da ya yi nufin yi, na filayen Haikalin Ubangiji da dukan ɗakuna na kewaye, da ɗakunan ajiya na Haikalin Allah, da ɗakunan ajiye kyautan da aka keɓe ga Ubangiji.
13. Ya kuma ba shi tsarin ƙungiyoyin firistoci da na Lawiyawa, da na dukan hidimar da za a yi a Haikalin Ubangiji, da aikin lura da kayayyakin aiki na cikin Haikalin Ubangiji.