Ya kuma ba shi tsarin dukan abin da ya yi nufin yi, na filayen Haikalin Ubangiji da dukan ɗakuna na kewaye, da ɗakunan ajiya na Haikalin Allah, da ɗakunan ajiye kyautan da aka keɓe ga Ubangiji.