9. Waɗansu kuwa za su amsa su ce, ‘Saboda sun bar bin Ubangiji Allahnsu wanda ya fito da kakanninsu daga ƙasar Masar, suka bi waɗansu gumaka, suka yi musu sujada, suka bauta musu, domin haka Ubangiji ya ɗora musu wannan masifa.’ ”
10. Sulemanu ya yi shekara ashirin kafin ya gama ginin Haikalin Ubangiji da fādarsa.
11. Hiram, Sarkin Taya, kuwa ya ba Sulemanu katakan itacen al'ul da na fir da zinariya, iyakar yadda yake bukata. Sarki Sulemanu kuwa ya ba Hiram garuruwa ashirin a jihar Galili.
12. Amma sa'ad da Hiram ya zo daga Taya domin ya ga garuruwan da Sulemanu ya ba shi, sai ya ga ba su gamshe shi ba.
13. Don haka ya ce wa Sulemanu, “Dan'uwa, waɗanne irin garuruwa ke nan da ka ba ni?” Saboda haka har yanzu ana kiran ƙasar Kabul, wato marar amfani.
14. Hiram kuma ya aika wa Sulemanu da zinariya mai nauyin talanti ɗari da ashirin.
15. Wannan shi ne lissafin aikin tilas da sarki Sulemanu ya sa domin ginin Haikalin, da na fādarsa, da kuma Millo, a kuma gina garun birnin. Ya kuma sa tilas a sāke gina garuruwan Hazor, da Magiddo, da Gezer.
16. Gama Fir'auna ya haura, ya ci Gezer, ya ƙone ta da wuta, ya kuma kashe masu zama cikinta. Sa'an nan ya yi wa 'yarsa, wato matar Sulemanu, kyauta da Gezer ɗin.
17. Sulemanu kuwa ya sāke gina Gezer. Ya kuma sa aka gina Bet-horon ta kwari ta aikin tilas,
18. da Ba'alat, da Tadmor a cikin jeji, a ƙasar Yahuza,
19. da garuruwan ajiyarsa, da garuruwan karusansa, da garuruwan mahayan dawakansa, da duk abin da Sulemanu ya so ya gina a Urushalima, da Lebanon, da dukan ƙasar da ya mallaka.