15. Sai ya tara sojoji matasa na hakiman larduna, mutum ɗari biyu da talatin da biyu. Sa'an nan kuma, ya tara dukan mutanen Isra'ila dubu bakwai (7,000).
16. Suka tafi da tsakar rana sa'ad da Ben-hadad yake a buge da sha a sansani, shi da sarakuna talatin da biyu waɗanda suka taimake shi.
17. Samarin ne suka fara fita. Sai Ben-hadad ya aiki mutane, suka faɗa masa cewa, “Mutane suna zuwa daga Samariya.”
18. Sai ya ce, “Ku kama su da rai, ko sun zo da nufin salama ko da na yaƙi.”
19. Waɗannan kuwa suka fita daga birnin, wato sojoji matasa, rundunar Isra'ilawa kuma tana biye da su,
20. kowa ya kashe abokin gābansa. Suriyawa kuwa suka gudu, Isra'ilawa kuma suka runtume su. Amma Ben-hadad, Sarkin Suriya, ya tsere kan doki tare da mahayan dawakai.
21. Sarkin Isra'ila ya fita, ya ƙwace dawakai da karusai, ya kashe Suriyawa da yawa.
22. Sa'an nan annabin ya je wurin Sarkin Isra'ila, ya ce masa, “Tafi, ka ƙarfafa kanka, ka yi tunani sosai a kan abin da za ka yi, gama da juyawar shekara Sarkin Suriya zai kawo maka yaƙi.”
23. Fādawan Sarkin Suriya suka ce masa, “Allolinsu na tuddai ne, don haka suka fi mu ƙarfi, bari mu yi yaƙi da su a cikin kwari, ta haka za mu ci su ba shakka.
24. Yanzu abin da za ka yi ke nan, sai ka fitar da sarakuna daga matsayinsu, ka sa shugabannin sojoji maimakonsu.
25. Sa'an nan ka tara sojoji kamar yawan waɗanda ka rasa, ka kuma tara dawakai a maimakon na dā, da karusai a maimakon karusai na dā. Mu kuwa za mu yi yaƙi da su a kwari. Ba shakka za mu ci su.”Sarki Ben-hadad ya ji maganarsu, ya kuwa yi haka nan.