7. Ubangiji kuma ya yi magana da Yehu ɗan Hanani, a kan Ba'asha da gidansa, saboda muguntar da ya aikata a gaban Ubangiji, har ya sa Ubangiji ya yi fushi, gama abin da ya aikata ya yi daidai da na Yerobowam, saboda kuma ya hallaka gidan Yerobowam.
8. A shekara ta ashirin da shida ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza, Ila ɗan Ba'asha, ya ci sarautar Isra'ila a Tirza. Ya yi sarauta shekara biyu.
9. Amma Zimri, shugaban rabin karusan Ila, ya yi masa maƙarƙashiya. Sa'ad da Ila yake Tirza, ya sha, ya bugu a gidan Arza wanda yake lura da fāda,
10. sai Zimri ya shiga gidan, ya buge shi ya kashe shi. Wannan ya faru a shekara ta ashirin da bakwai ta sarautar Asa, Sarkin Yahuza.
11. Da Zimri ya zama sarki, nan da nan sai ya kashe dukan mutanen gidan Ba'asha, bai bar masa wani namiji, ko dangi, ko aboki ba.
12. Haka Zimri ya hallaka gidan Ba'asha bisa ga maganar da Ubangiji ya faɗa a kansa ta bakin annabi Yehu.
13. Wannan kuwa ya faru saboda zunuban Ba'asha da na ɗansa Ila, da zunuban da suka sa jama'ar Isra'ila su yi, har suka sa Ubangiji Allah na Isra'ila ya yi fushi saboda gumakansu.
14. Sauran ayyukan Ila da dukan abin da ya yi an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Isra'ila.