5. domin Dawuda ya aikata abu mai kyau a gaban Ubangiji. Bai ƙetare umarnin da Ubangiji ya ba shi ba dukan kwanakin ransa, sai dai a kan Uriya Bahitte.
6. Akwai yaƙi tsakanin Abaija da Yerobowam dukan kwanakin ransa.
7. Sauran ayyukan Abaija da dukan abin da ya aikata, an rubuta su a littafin tarihin sarakunan Yahuza.
8. Abaija ya rasu, suka binne shi a Urushalima. Ɗansa Asa ya gāji sarautarsa.
9. A cikin shekara ta ashirin ta sarautar Yerobowam Sarkin Isra'ila, Asa ya sarauci jama'ar Yahuza.
10. Ya yi shekara arba'in da ɗaya yana sarauta a Urushalima. Sunan tsohuwarsa Ma'aka, 'yar Absalom, wato kakarsa.
11. Asa kuwa ya aikata abin da yake daidai a gaban Ubangiji kamar yadda kakansa, Dawuda, ya yi.
12. Ya kori mata da maza da suke karuwanci a wuraren tsafi na arna a ƙasar, ya kuma kawar da gumakan da kakanninsa suka yi.
13. Ya kuma fitar da tsohuwarsa Ma'aka daga zaman sarauniya, domin ta yi ƙazantacciyar siffa ta gunkiyar Ashtoret. Asa ya sassare siffar, ya ƙone ta a rafin Kidron.