1 Sar 11:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sarki Sulemanu ya ƙaunaci baƙin mata. Banda 'yar Fir'auna, Sarkin Masar, ya auri matan Mowabawa, da na Ammonawa, da na Edomawa, da na Sidoniyawa, da na Hittiyawa.

2. Suna kuwa cikin al'umman da Ubangiji ya umarci jama'ar Isra'ila, ya ce, “Kada ku yi aurayya da su, gama hakika za su karkatar da zuciyarku zuwa gumakansu.” Sulemanu kuwa ya manne wa waɗannan mata da yake ƙauna.

3. Ya auri mata ɗari bakwai, dukansu kuwa gimbiyoyi ne. Yana kuma da ƙwaraƙwarai ɗari uku. Matan nan nasa kuwa suka janye zuciyarsa daga bin Ubangiji,

4. sa'ad da Sulemanu ya tsufa sai suka janye zuciyarsa zuwa bin waɗansu gumaka, bai bi Ubangiji Allahnsa da zuciya ɗaya kamar yadda tsohonsa, Dawuda, ya yi ba.

5. Gama Sulemanu ya bi Ashtoret ta Sidoniyawa, da Milkom, wato gunkin Ammonawa.

6. Ya yi wa Ubangiji zunubi. Bai bi Ubangiji da zuciya ɗaya kamar yadda tsohonsa, Dawuda, ya yi ba.

7. Sulemanu ya gina wa Kemosh, wato gunkin Mowab, da Molek, gunkin Ammonawa, masujadai a kan dutsen da yake gabas da Urushalima.

8. Ya kuma gina masujadai inda dukan matansa baƙi za su riƙa miƙa turare da hadayu ga gumakansu.

9. Ubangiji kuwa ya yi fushi da Sulemanu, domin zuciyar Sulemanu ta rabu da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda ya bayyana a gare shi sau biyu,

10. ya kuma umarce shi kada ya bi gumaka. Amma bai kiyaye umarnin da Ubangiji ya yi masa ba.

11. Saboda haka Ubangiji ya ce wa Sulemanu, “Tun da yake ka yi haka, ba ka kuwa kiyaye umarnina da dokokina waɗanda na umarce ka da su ba, to, hakika zan ƙwace mulki daga gare ka, in ba baranka.

12. Amma saboda tsohonka, Dawuda, ba zan ƙwace a zamaninka ba, amma zan ƙwace daga hannun ɗanka.

1 Sar 11