1 Sam 6:11-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Suka sa akwatin alkawarin Ubangiji a keken, da akwatin siffofin ɓerayen zinariya da siffofin maruran.

12. Shanun kuwa suka kama hanya sosai wadda ta nufi wajen Bet-shemesh, suna tafe, suna ta kuka, ba su kauce zuwa dama ko hagu ba, sarakunan Filistiyawa suna biye da su, har zuwa iyakar Bet-shemesh.

13. Mutanen Bet-shemesh kuwa suna cikin yankan alkamarsu a kwari. Da suka ɗaga kai sai suka ga akwatin alkawari, sai suka yi murna matuƙa.

14. Keken shanun kuwa ya shiga gonar Joshuwa mutumin Bet-shemesh, ya tsaya a wurin, kusa da wani babban dutse. Mutanen suka faskare keken shanun, suka yanka shanun suka ƙone su hadaya ga Ubangiji.

15. Lawiyawa kuwa suka ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji da akwatin da yake gefensa wanda aka sa siffofin zinariya a ciki. Suka ajiye su a kan babban dutsen. Mutanen Bet-shemesh kuwa suka miƙa wa Ubangiji hadaya ta ƙonawa da waɗansu hadayu kuma a wannan rana.

16. Sarakunan nan biyar na Filistiyawa sun ga an yi wannan, sa'an nan suka koma Ekron a ran nan.

17. Waɗannan su ne siffofin marurai na zinariya waɗanda Filistiyawa suka aika domin yin hadaya don laifi ga Ubangiji, ɗaya domin Ashdod, ɗaya domin Gaza, ɗaya domin Ashkelon, ɗaya domin Gat, ɗaya kuma domin Ekron.

18. Suka kai siffofin ɓerayen nan na zinariya kuwa domin garuruwa biyar masu garu da ƙauyuka marasa garu na sarakunan Filistiyawa. Babban dutse inda suka ajiye akwatin Ubangiji yana nan har wa yau a saurar Joshuwa Bet-shemesh.

19. Sai Ubangiji ya kashe mutum saba'in daga cikin mutanen Bet-shemesh domin sun leƙa cikin akwatin alkawari na Ubangiji. Mutanen kuwa suka yi makoki ƙwarai domin Ubangiji ya kashe mutane da yawa daga cikinsu.

20. Mutanen Bet-shemesh suka ce, “Wa ya isa ya tsaya a gaban Ubangiji, Allahn nan mai tsarki? A wurin wa zai tafi don ya rabu da mu?”

21. Sai suka aiki manzanni wurin mutanen Kiriyat-yeyarim, suka ce, “Filistiyawa sun komo da akwatin alkawari na Ubangiji, sai ku zo, ku ɗauka, ku tafi da shi.”

1 Sam 6