Shanun kuwa suka kama hanya sosai wadda ta nufi wajen Bet-shemesh, suna tafe, suna ta kuka, ba su kauce zuwa dama ko hagu ba, sarakunan Filistiyawa suna biye da su, har zuwa iyakar Bet-shemesh.