9. saboda haka Eli ya ce wa Sama'ila ya koma ya kwanta, idan an sāke kiransa sai ya ce, “Ya Ubangiji, ka yi magana, gama bawanka yana kasa kunne.” Sama'ila kuwa ya koma ya kwanta.
10. Ubangiji kuma ya zo ya tsaya, ya yi kira kamar dā, ya ce, “Sama'ila! Sama'ila!”Sama'ila ya amsa ya ce, “Ka yi magana, gama bawanka yana kasa kunne.”
11. Sa'an nan Ubangiji ya ce wa Sama'ila, “Zan yi wa Isra'ilawa wani abu, duk wanda ya ji kuwa zai razana.
12. A ranar zan cika abin da na faɗa game da Eli da iyalinsa daga farko har zuwa ƙarshe.
13. Na fāɗa masa zan hukunta gidansa har abada saboda 'ya'yansa sun faɗi mugayen maganganu a kaina. Eli kuwa ya sani, amma bai kwaɓe su ba.
14. Domin haka na faɗa da ƙarfi, cewa laifin gidan Eli ba za a yi kafararsa da sadaka, ko da hadaya ba har abada.”
15. Sama'ila ya kwanta har safiya, sa'an nan ya buɗe ƙofofi. Amma ya ji tsoron faɗa wa Eli wahayin.
16. Amma Eli ya kira shi, ya ce, “Ya ɗana, Sama'ila.”Sama'ila ya ce, “Ga ni.”
17. Eli ya tambaye shi, ya ce, “Me Ubangiji ya faɗa maka? Kada ka ɓoye mini. Allah zai hukunta ka idan ka ɓoye mini abin da ya faɗa maka.”
18. Sama'ila kuwa ya faɗa masa kome da kome, bai ɓoye masa kome ba. Sai Eli ya ce, “Ai, Ubangiji ne, bari ya yi abin da ya yi masa daidai.”