1. Yaron nan Sama'ila yana yi wa Ubangiji aiki a hannun Eli. A lokacin nan Ubangiji bai cika yin magana da mutane ba, ba safai kuma ake samun wahayi ba.
2. Wata rana da dare Eli wanda ya kusa makancewa har ba ya iya gani sosai, yana kwance a masujada.
3. Fitilar Ubangiji kuwa tana ci. Sama'ila kuma yana kwance a masujada inda akwatin alkawarin Allah yake.
4. Ubangiji kuwa ya kira Sama'ila. Sama'ila ya ce, “Na'am.”
5. Ya sheƙa zuwa wurin Eli, ya ce, “Ga ni, gama ka kira ni.”Amma Eli ya ce masa, “Ban kira ka ba, koma ka kwanta.” Sai Sama'ila ya koma ya kwanta.