1 Sam 24:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Da Saul ya komo daga yaƙi da Filistiyawa, sai aka faɗa masa Dawuda yana jejin En-gedi.

2. Sai Saul ya zaɓi mutum dubu uku (3,000) daga cikin dukan mutanen Isra'ila, ya tafi ya nemi Dawuda da mutanensa a gaban duwatsun awakin jeji.

3. Saul ya isa garken tumaki a gefen hanya, inda akwai kogo. Sai ya shiga cikin kogon don ya huta. Dawuda da mutanensa kuwa suna zaune a ƙurewar kogon.

4. Mutanen Dawuda suka ce masa, “Wannan ita ce ranar da Ubangiji ya ba da maƙiyinka a hannunka, ka yi yadda ka ga dama da shi.” Dawuda kuwa ya tashi a hankali, ya yanke shafin rigar Saul.

5. Daga baya zuciyar Dawuda ta kāshe shi domin ya yanke shafin rigar Saul.

6. Ya ce wa mutanensa, “Ubangiji ya sawwaƙa in yi wa ubangijina irin abu haka, har in miƙa hannuna in kashe keɓaɓɓe na Ubangiji.”

7. Da wannan magana Dawuda ya rinjayi mutanensa, bai yarda musu su fāɗa wa Saul ba.Sai Saul ya fita daga kogon ya kama hanya, ya yi tafiyarsa.

8. Daga baya kuma Dawuda ya fita daga kogon, ya yi kira, ya ce, “Ya ubangijina, sarki.” Da Saul ya waiwaya, sai Dawuda ya rusuna.

9. Ya ce wa Saul, “Me ya sa kake kasa kunne ga maganganun mutanen da suke cewa, ‘Dawuda yana nema ya cuce ka?’

1 Sam 24