Saul ya isa garken tumaki a gefen hanya, inda akwai kogo. Sai ya shiga cikin kogon don ya huta. Dawuda da mutanensa kuwa suna zaune a ƙurewar kogon.