16. Don ko da yake ina yin bishara, ba na fahariya da haka, gama tilas ne a gare ni. Kaitona in ba na yin bishara!
17. Da da ra'ina nake yi, da sai a biya ni. Amma da yake ba da ra'ina ba ne, an danƙa mini amana ke nan.
18. Ina kuma hakkina? To, ga shi. A duk lokacin da nake yin bishara, sona in yi ta a kyauta, kada in ƙurashe halaliyata a game da bishara.
19. Ko da yake ni ba bawan kowa ba ne, na mai da kaina bawan kowa, domin in rinjayi mutane masu yawa.
20. Ga Yahudawa, sai na zama kamar Bayahude, domin in rinjayi Yahudawa. Ga waɗanda Shari'a take iko da su, sai na zama kamar wanda Shari'a take iko da shi, ko da yake ba Shari'a take iko da ni ba, domin in rinjayi waɗanda Shari'a take iko da su ne.
21. Ga marasa Shari'a kuwa, sai na zama kamar marar Shari'a, ba cewa ba wata shari'ar Allah da take iko da ni ba, a'a, shari'ar Almasihu na iko da ni, domin in rinjayi marasa Shari'a ne.
22. Ga raunana, sai na zama kamar rarrauna domin in rinjayi raunana. Na zama kowane irin abu ga ko waɗanne irin mutane, domin ta ko ƙaƙa in ceci waɗansu.
23. Na yi wannan ne duk saboda bishara, domin in sami rabo a cikin albarkarta.
24. Ashe, ba ku sani ba, a wajen tsere dukan masu gudu suna ƙoƙarin tsere wa juna, amma ɗaya ne kaɗai yake samun kyautar ci? To, sai ku yi ta gudu haka nan, don ku ci.