7. Ku yi ƙarar juna ma, ai, hasara ce a gare ku. Ba gara ku haƙura a cuce ku ba? Ku kuma haƙura a zambace ku?
8. Amma, ga shi, ku da kanku kuna cuta, kuna zamba, har ma 'yan'uwanku kuke yi wa!
9. Ashe, ba ku sani ba, marasa adalci ba za su sami gādo a cikin Mulkin Allah ba? Kada fa a yaudare ku! Ba fasikai, ko matsafa, ko mazinata, ko masu luɗu da maɗugo,
10. ko ɓarayi, ko makwaɗaita, ko mashaya, ko masu zage-zage, ko mazambata, da za su sami gādo a cikin Mulkin Allah.
11. Waɗansunku ma dā haka suke, amma an wanke ku, an tsarkake ku, an kuma kuɓutar da ku, da sunan Ubangiji Yesu Almasihu, da kuma Ruhun Allahnmu.
12. “Dukan abubuwa halal ne a gare ni,” amma ba dukan abubuwa ne masu amfani ba. “Abu duka halal na a gare ni,” amma ba zan zama bawan kome ba.
13. “Abinci don ciki aka yi shi, ciki kuma don abinci”–Allah kuma zai hallaka duka biyu, wannan da wancan. Jiki kam, ba don fasikanci yake ba, sai dai domin Ubangiji, Ubangiji kuma domin jiki.
14. Allah ya ta da Ubangiji daga matattu, haka mu ma zai ta da mu da ikonsa.
15. Ashe, ba ku sani ba jikinku gaɓoɓin Almasihu ne? Ashe kuma, sai in ɗauki gaɓoɓin Almasihu in mai da su gaɓoɓin karuwa? Faufau!
16. Ashe, ba ku sani ba, duk wanda ya tara da karuwa, sun zama jiki ɗaya ke nan? Domin a rubuce yake cewa, “Su biyun za su zama jiki ɗaya.”
17. Duk wanda kuwa yake haɗe da Ubangiji, sun zama ɗaya a ruhu ke nan.
18. Ku guji fasikanci. Duk sauran zunubin da mutum yake yi bai shafi jikinsa ba, amma mai yin fasikanci, yana ɗaukar alhalin jikinsa ne.