1. A watan takwas a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus, Ubangiji ya yi magana da annabi Zakariya, ɗan Berekiya, ɗan Iddo, ya ce,
2. “Ubangiji ya yi fushi da kakanninku.
3. Domin haka sai ka ce musu, Ubangiji Mai Runduna ya ce, ‘Ku komo wurina, ni kuma zan komo wurinku, ni Ubangiji Mai Runduna na faɗa.’
4. Kada ku zama kamar kakanninku, waɗanda annabawa na dā suka yi ta yi musu shela suna cewa, ‘Ubangiji Mai Runduna ya ce, ku bar mugayen hanyoyinku da mugayen ayyukanku.’ Amma ba su ji ba, ba su kuwa kula ba, ni Ubangiji na faɗa.
5. To, ina kakannin nan naku suke? Annabawan fa? Suna da rai har wa yau?
6. Amma maganata da dokokina waɗanda na umarta wa bayina annabawa, sun tabbata a kan kakanninku, sai suka tuba, suka ce, ‘Kamar yadda Ubangiji Mai Runduna ya yi niyya ya yi da mu saboda hanyoyinmu da ayyukanmu, haka kuwa ya yi da mu.’ ”
7. A rana ta ashirin da huɗu ga watan goma sha ɗaya, wato watan Shebat, a shekara ta biyu ta sarautar Dariyus, Ubangiji ya kuma yi magana da annabi Zakariya, ɗan Berekiya, ɗan Iddo.
8. Da dare, na ga mutum yana kan aharashin doki, yana tsaye a cikin itatuwan ci-zaƙi, a kwari. A bayansa kuma ga wani aharashin doki, da bidi, da kili.
9. Sai na ce, “Mene ne waɗannan, ya Ubangiji?”Mala'ikan da ya yi magana da ni ya ce, “Zan bayyana maka ma'anarsu.”
10. Sai mutumin da yake tsaye a cikin itatuwan ci-zaƙin ya amsa ya ce, “Waɗannan su ne Ubangiji ya aike su su yi tsaron duniya, suna kai da kawowa.”