Zab 5:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ka kasa kunne ga kalmomina, ya Ubangiji,Ka kuma ji ajiyar zuciyata.

2. Ya Sarkina, Allahna,Ka kasa kunne ga kukana na neman taimako.

3. A gare ka zan yi addu'a, ya Ubangiji,Da safe za ka ji muryata,Da hantsi zan yi addu'ata,In kuma jira amsa.

4. Kai ba Allah mai yarda da aikin kuskure ba ne,Ba ka yarda da mugunta a gabanka.

5. Ba ka jurewa da ganin mutane masu fāriya,Kana ƙin mugaye.

6. Kakan hallakar da duk maƙaryata,Kakan raina masu ta da hankali da masu ruɗi.

7. Amma ni, ina iya zuwa wurinka,Saboda ƙaunarka mai girma,In yi sujada a tsattsarkan Haikalinka,In kuma rusuna maka da bangirma.

8. Ina da abokan gāba da yawa, ya Ubangiji,Ka bi da ni in aikata nufinka,Ka kuma fayyace mini hanyarka domin in bi ta!

9. Abin da maƙiyana ke faɗa,Ba abin da za a yarda da shi ba ne,Su dai, so suke su hallakar kawai,Bakinsu kamar buɗaɗɗen kabari yake,Maganganunsu kuwa suna da taushi da kuma yaudara.

Zab 5