Zab 45:2-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Kai ne mafi kyau a cikin dukan mutane,Kai mai kyakkyawan lafazi ne,Kullum Allah yakan sa maka albarka!

3. Ka sha ɗamara da takobinka, ya Maɗaukakin Sarki,Kai mai iko ne, Maɗaukaki!

4. Ka yi hawan ɗaukaka zuwa nasara,Domin ka tsare gaskiya da adalci.Saboda ikonka za ka yi babban rinjaye.

5. Kibanka suna da tsini,Suna huda zuciyar abokan gābanka,Al'ummai suna fāɗuwa ƙasa a ƙafafunka.

6. Kursiyinka, ya Allah, zai dawwama har abada abadin!Kana mulkin mallakarka da adalci.

7. Kana ƙaunar abin da yake daidai,Kana ƙin abin da yake mugu.Saboda haka Allah, Allahnka, ya zaɓe ka,Ya kuwa kwararo maka farin ciki mai yawa fiye da kowa.

8. Tufafinka suna ƙanshin turaren mur, da na aloyes, da na kashiya,A kowace fādar hauren giwa, mawaƙa suna yi maka waƙar.

Zab 45