1. Kwanyata ta cika da kyawawan kalmomi,Lokacin da nake tsara waƙar sarki,Harshena kuwa kamar alkalami ne na ƙwararren marubuci.
2. Kai ne mafi kyau a cikin dukan mutane,Kai mai kyakkyawan lafazi ne,Kullum Allah yakan sa maka albarka!
3. Ka sha ɗamara da takobinka, ya Maɗaukakin Sarki,Kai mai iko ne, Maɗaukaki!
4. Ka yi hawan ɗaukaka zuwa nasara,Domin ka tsare gaskiya da adalci.Saboda ikonka za ka yi babban rinjaye.
5. Kibanka suna da tsini,Suna huda zuciyar abokan gābanka,Al'ummai suna fāɗuwa ƙasa a ƙafafunka.