Zab 29:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ku yabi Ubangiji, ku alloli,Ku yabi ɗaukakarsa da ikonsa.

2. Ku yabi sunan Ubangiji mai daraja,Ku rusuna a gaban Mai Tsarki sa'ad da ya bayyana.

3. An ji muryar Ubangiji a kan tekuna,Allah Maɗaukaki ya yi tsawa,Tsawar muryarsa kuwa ta yi amsa kuwa a bisa teku.

4. An ji muryar UbangijiA dukan ikonsa da zatinsa!

5. Muryar Ubangiji takan karya itatuwan al'ul,Har ma da itatuwan al'ul na Lebanon.

6. Yakan sa duwatsun Lebanon su yi tsalle kamar 'yan maruƙa,Ya kuma sa Dutsen Harmon ya yi tsalle kamar ɗan maraƙi.

7. Muryar Ubangiji ta sa walƙiya ta walƙata.

Zab 29