Yush 2:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Za ta bi samarinta, amma ba za ta tarar da su ba.Za ta neme su, amma ba za ta same su ba.Sa'an nan za ta ce, ‘Zan koma wurin mijina na fari,Gama zamana na dā ya fi na yanzu!’

8. “Amma ba ta sani ni nake ba ta hatsi, da ruwan inabi, da mai,Da azurfa, da zinariya da yawaWaɗanda suka bauta wa gunkin nan Ba'al da su ba.

9. Don haka zan hana mata hatsi a kakarsa,Da ruwan inabi a kakarsa, da kuma ulu da lilinWaɗanda suka zama abin rufe tsiraicinta.

10. Yanzu zan buɗe tsiraicintaA idon samarinta,Ba kuwa wanda zai cece ta daga hannuna.

11. Zan sa ta daina farin cikinta,Da idodinta, da kiyaye lokatan amaryar wata,Da hutawar ranar Asabar,Da ƙayyadaddun idodinta.

12. Zan ɓata inabinta da itatuwan ɓaureWaɗanda take cewa, ‘Waɗannan su ne hakkinaWanda samarina suka ba ni.’Zan sa su zama kurmi,Namomin jeji su cinye su.

13. Zan hukunta ta saboda kwanakin idodin gunkin nan Ba'al.A kwanakin nan takan ƙona musu turare,Ta yi ado da zobe da lu'ulu'ai,Ta bi samarinta, amma ta manta da ni.”In ji Ubangiji.

14. “Don haka, ga shi, zan rarrashe ta,In kai ta cikin jeji,In ba ta magana.

15. Can zan ba ta gonar inabi,In mai da kwarin Akor, wato wahala, ƙofar bege.A can za ta amsa mini kamar a kwanakin ƙuruciyarta,Kamar lokacin da ta fito daga ƙasar Masar.

16. Ni Ubangiji na ce, a waccan ranaZa ta ce da ni,‘Mijina,’ ba za ta ƙara ce da ni Ba'al ba.

17. Zan kawar da sunayen Ba'al daga bakinta.Ba za a ƙara kiransu da sunayensu ba.

Yush 2