Yush 14:4-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Ubangiji ya ce, “Zan warkar musu da riddarsu.Zan kuma ƙaunace su sosai,Gama fushina zai huce.

5. Zan zama kamar raɓa ga Isra'ila,Isra'ila za ta yi fure kamar lili,Saiwarta za ta shiga kamar itacen al'ul.

6. Tohonta zai buɗo,Kyanta zai zama kamar itacen zaitun,Ƙashinta kuwa kamar itacen al'ul na Lebanon.

7. Waɗanda za su komo, za su zauna a inuwarta,Za su yi noman hatsi da yawa.Za su yi fure kamar kurangar inabi.Ƙanshinsu zai zama kamar ruwan inabi na Lebanon.

8. Ya mutanen Ifraimu, me zan yi da gumaka?Ni ne wanda yake amsa muku, mai lura da ku kuma.Ni kamar itacen fir ne mai ganyaye kore shar.Daga gare ni, kuke samun 'ya'ya.”

Yush 14