1. Ya mutanen Isra'ila, ku komo wurin Ubangiji Allahnku,Gama zunubinku ya sa kun yi tuntuɓe.
2. Ku komo wurin Ubangiji, ku roƙe shi,Ku ce, “Ka gafarta mana zunubanmu,Ka karɓe mu saboda alherinka,Mu kuwa za mu yabe ka da bakinmu.
3. Assuriya ba za ta cece mu ba,Ba kuwa za mu hau dawakai ba.Ba za mu kuma ƙara ce da aikin hannuwanmu,‘Kai ne Allahnmu,’ ba.A wurinka ne maraya yakan sami jinƙai.”
4. Ubangiji ya ce, “Zan warkar musu da riddarsu.Zan kuma ƙaunace su sosai,Gama fushina zai huce.
5. Zan zama kamar raɓa ga Isra'ila,Isra'ila za ta yi fure kamar lili,Saiwarta za ta shiga kamar itacen al'ul.