Yun 3:4-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Sai Yunusa ya kama tafiya yana ratsa birnin, da ya yi tafiyar yini guda, sai ya yi shela ya ce, “Nan da kwana arba'in za a hallaka Nineba.”

5. Sai mutanen Nineba suka gaskata Allah, suka tsai da shawara, cewa kowa da kowa ya yi azumi. Dukan mutane kuwa babba da yaro, suka sa tufafin makoki.

6. Sa'ad da Sarkin Nineba ya ji labarin, sai ya sauka daga kursiyinsa, ya tuɓe rigarsa, ya sa rigar makoki, ya zauna cikin toka.

Yun 3