14. Ku sa a yi azumi,Ku kira muhimmin taro.Ku tara dattawa da dukan mutanenƙasarA Haikalin Ubangiji Allahnku,Ku yi kuka ga Ubangiji.
15. Taku ta ƙare a wannan rana!Gama ranar Ubangiji ta kusa,Halaka daga wurin Maɗaukaki ta zo.
16. An lalatar da amfanin gonaki a kanidonmu,Ba murna a Haikalin Allahnmu.
17. Itatuwa sun mutu a busasshiyarƙasa,Ba hatsin da za a adana a rumbu,Rumbuna sun lalace domin ba hatsi.
18. Dabbobi suna nishi!Garkunan shanu sun ruɗeDomin ba su da makiyaya.Garkunan tumaki da awaki kumasuna shan azaba.
19. Ina kuka a gare ka, ya Ubangiji,Domin ciyayi da itatuwa sun bushe,Sai ka ce wuta ce ta ƙone su.
20. Har ma namomin jeji suna kuka agare ka,Domin rafuffuka sun bushe,Ciyayi kuma sun bushe,Sai ka ce wuta ce ta ƙone su.