28. Sai matar ta bar tulunta, ta koma gari, ta ce wa mutane,
29. “Ku zo, ku ga mutumin da ya gaya mini duk abin da na taɓa yi! Shin, ko wannan shi ne Almasihu?”
30. Sai suka fito daga garin suka nufo shi.
31. Ana cikin haka sai almajiran suka roƙe shi suka ce, “Ya shugaba, ci abinci.”
32. Amma ya ce musu, “Ina da abincin da ba ku sani ba.”
33. Almajiran suka ce wa juna, “Shin, wani ya kawo masa abinci ne?”
34. Sai Yesu ya ce musu, “Abincina shi ne in aikata nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa.
35. Ba kuna cewa, kaka saura wata huɗu ba? Ina gaya muku fa, ku duba gonaki, ku gani, sun nuna sun isa girbi.
36. Mai girbi na samun lada, yana kuma tara amfani zuwa rai madawwami, domin mai shuka da mai girbi su yi farin ciki tare.
37. A nan kam, wannan karin maganar gaskiya ne cewa, ‘Wani da shuka, wani da girbi.’
38. Na aike ku girbin abin da ba ku yi wahalarsa ba. Waɗansu sun yi wahala, ku kuwa kun mori wahalarsu.”
39. Samariyawa da yawa na wannan gari suka gaskata da shi saboda maganar matan nan da ta ce, “Ya gaya mini duk abin da na taɓa yi.”
40. Da Samariyawa suka iso wurinsa, suka roƙe shi ya sauka a wurinsu. Ya kuwa kwana biyu a nan.
41. Waɗansu kumma da yawa fiye da na dā suka ba da gaskiya saboda magana tasa.
42. Sa'an nan suka ce wa macen, “Yanzu kam, mun ba da gaskiya, ba don abin da kika faɗa kawai ba, domin mu ma mun ji da kanmu, mun kuma tabbata lalle wannan shi ne Mai Ceton duniya.”
43. Bayan kwana biyun nan sai ya tashi daga nan ya tafi ƙasar Galili.
44. Domin Yesu kansa ya yi shaida cewa annabi ba shi da girma a ƙasarsu.
45. Da ya isa ƙasar Galili, sai Galilawa suka yi na'am da shi, domin sun ga duk abin da ya yi a Urushalima a lokacin idi, domin su ma sun je idin.