Yah 19:29-42 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. To, akwai wani gora cike da ruwan tsami a ajiye a nan. Sai suka jiƙa soso da ruwan tsamin, suka soka a sandan izob suka kai bakinsa.

30. Da Yesu ya tsotsi ruwan tsamin nan ya ce, “An gama!” Sa'an nan ya sunkuyar da kansa ya ba da ransa.

31. Da yake ran nan ranar shiri ce, don kada a bar jikuna a gicciye ran Asabar (domin wannan Asabar ɗin babbar rana ce), sai Yahudawa suka roƙi Bilatus a karya ƙafafunsu, a kuma ɗauke jikunan.

32. Sai soja suka zo suka karya ƙafafun na farkon nan, da kuma na ɗayan da aka gicciye tare da shi.

33. Amma da suka zo wurin Yesu, suka kuma ga ya riga ya mutu, ba su karya ƙafafunsa ba.

34. Sai dai ɗaya daga cikin sojan nan ya soke shi da mashi a kwiɓi, nan da nan sai ga jini da ruwa suka gudano.

35. Wanda ya gani ɗin kuwa shi ya ba da shaida kan haka, shaida tasa kuwa gaskiya ce, ya kuma san gaskiya yake faɗa, domin ku ma ku ba da gaskiya.

36. Wannan kuwa don a cika Nassi ne cewa, “Ƙashinsa ɗaya ba za a karya ba.”

37. Wani Nassi kuma ya ce, “Za su dubi wanda suka soka.”

38. Bayan haka Yusufu, mutumin Arimatiya, wanda yake almajirin Yesu ne amma a ɓoye domin tsoron Yahudawa, ya roƙi Bilatus izinin ɗauke jikin Yesu. Bilatus kuwa ya ba shi izini, ya kuwa zo ya ɗauke jikin Yesu.

39. Nikodimu kuma, wanda farkon zuwansa wurin Yesu da dad dare ne, ya zo da mur da al'ul a gauraye, wajen awo ɗari.

40. Sai suka ɗauki jikin Yesu suka sa shi a likkafanin lilin game da kayan ƙanshin nan, bisa ga al'adar Yahudawa ta jana'iza.

41. A wurin da aka gicciye shi kuwa akwai wani lambu, a cikin lambun kuma da wani sabon kabari wanda ba a taɓa sa kowa ba.

42. Da yake ranar shiri ce ta Yahudawa, kabarin kuma na kusa, sai suka sa Yesu a nan.

Yah 19