Yah 19:38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Bayan haka Yusufu, mutumin Arimatiya, wanda yake almajirin Yesu ne amma a ɓoye domin tsoron Yahudawa, ya roƙi Bilatus izinin ɗauke jikin Yesu. Bilatus kuwa ya ba shi izini, ya kuwa zo ya ɗauke jikin Yesu.

Yah 19

Yah 19:34-42