1. Idin Ƙetarewa sauran kwana shida, sai Yesu ya zo Betanya inda Li'azaru yake, wanda Yesu ya tasa daga matattu.
2. Nan aka yi masa abincin dare, Marta ce ta yi hidima, Li'azaru kuwa yana cikin masu ci tare da shi.
3. Sai Maryamu ta ɗauko awo guda na man ƙanshi na nardi tsantsa, mai tamanin gaske, ta shafa a ƙafafun Yesu, sa'an nan ta shafe su da gashinta. Duk gidan ya game da ƙanshin man.
4. Amma Yahuza Iskariyoti, ɗaya daga cikin almajiransa, wato wanda zai bāshe shi, ya ce,
5. “Me ya hana a sayar da man nan a kan dinari ɗari uku, a ba talakawa kuɗin?”
6. Ya faɗi haka fa, ba wai don yana kula da gajiyayyu ba, a'a, sai dai don shi ɓarawo ne, da yake kuma jakar kuɗinsu tana hannunsa, yakan riƙa taɓa abin da yake ciki.
7. Sai Yesu ya ce, “A ƙyale ta, dā ma ta ajiye shi domin tanadin ranar jana'izata.
8. Ai, kullum kuna tare da gajiyayyu, amma ba kullum kuke tare da ni ba.”
9. Da taron Yahudawa mai yawa suka ji labari yana nan, sai suka zo, ba domin Yesu kaɗai ba, har ma don su ga Li'azaru wanda ya tasa daga matattu.
10. Sai manyan firistoci suka yi shawarar kashe Li'azaru, shi ma,
11. domin ta dalilinsa Yahudawa da yawa suke warewa, suna gaskatawa da Yesu.