Yah 11:12-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. Sai almajiran suka ce masa, “Ya Ubangiji, in dai barci ne ya ɗauke shi, ai, zai warke.”

13. Alhali kuwa, Yesu zancen mutuwar Li'azaru yake, amma su sun ɗauka yana nufin barcin hutawa ne.

14. Sai Yesu ya gaya musu a fili, ya ce, “Li'azaru dai ya mutu.

15. Ina kuwa farin ciki da ba na nan, saboda ku domin ku ba da gaskiya. Amma mu dai je wurinsa.”

16. Sai Toma, wanda ake kira Ɗan Tagwai, ya ce wa 'yan'uwansa almajirai, “Mu ma mu tafi, mu mutu tare da shi.”

17. Da Yesu ya isa, ya tarar Li'azaru, har ya kwana huɗu a kabari.

18. Betanya kuwa kusa da Urushalima take, misalin mil biyu.

19. Yahudawa da yawa sun zo su yi wa Marta da Maryamu ta'aziyyar ɗan'uwansu.

20. Da jin Yesu na zuwa, sai Marta ta je taryensa, Maryamu kuwa ta zauna a gida.

21. Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, da kana nan da ɗan'uwana bai mutu ba.

22. Ko yanzu ma na sani kome ka roƙi Allah zai yi maka.”

23. Yesu ya ce mata, “Ɗan'uwanki zai tashi.”

24. Marta ta ce masa, “Na sani zai tashi a tashin matattu a ranar ƙarshe.”

25. Yesu ya ce mata, “Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu.

26. Wanda kuwa yake raye, yake kuma gaskatawa da ni, ba zai mutu ba har abada. Kin gaskata wannan?”

27. Ta ce masa, “I, ya Ubangiji. Na gaskata kai ne Almasihu, Ɗan Allah, shi wannan mai zuwa duniya.”

28. Da ta faɗi haka, ta je ta kirawo 'yar'uwa tata Maryamu, ta raɗa mata ta ce, “Ga Malam ya zo, yana kiranki.”

29. Ita kuwa da jin haka, ta yi maza ta tashi ta nufi wurinsa.

30. Yesu dai bai iso ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana wurin da Marta ta tarye shi.

31. Da Yahudawan da suke tare da ita a cikin gida, suna yi mata ta'aziyya, suka ga Maryamu ta yi maza ta tashi ta fita, suka bi ta, suna zaton za ta kabarin ne, ta yi kuka a can.

Yah 11