W. W. 4:13-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Shuke-shuke suna girma sosai.Suna girma kamar gonar itatuwan rumman.Suna ba da 'ya'ya mafi kyauDa kayan shafe-shafe kamar su lalle da nardi.

14. Nardi, da asfaran, da kalamus, da kirfa,Da dukan itatuwan da suke ba da kayan ƙanshi,Da mur, da aloyes, da dukan turare mafi ƙanshi.

15. Maɓuɓɓugai suna ba lambun ruwa, ruwan rafuffuka suna gudu,Ƙoramu suna bulbulo ruwa daga Dutsen Lebanon.

16. Farka, ya iskar arewa.Ki hura a kan lambuna, ke iskar kudu.Iska ta cika da ƙanshi.Bari ƙaunataccena ya zo lambunsa,Ya ci 'ya'yan itatuwa mafi kyau.

W. W. 4