Rom 12:7-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. in ta hidima ce, wajen hidimarmu, mai koyar da Maganar Allah kuwa, wajen koyarwarsa,

8. mai ƙarfafa zuciya kuwa, wajen ƙarfafawarsa, mai yin gudunmawa kuwa, yă bayar hannu sake, shugaba yă yi shugabancinsa da himma, mai yin aikin tausayi, yă yi shi da fara'a.

9. Ƙauna ta kasance sahihiya. Ku yi ƙyamar abin da yake mugu, ku lazamci abin da yake nagari.

10. A game da ƙaunar 'yan'uwa kuwa, ku ƙaunaci juna gaya. A wajen ba da girma, kowa yă riga ba ɗan'uwansa.

11. Kada ku sassauta a wajen himma, ku himmantu a ruhu, kuna bauta wa Ubangiji.

12. Sa zuciyar nan taku ta sa ku farin ciki, ku jure wa wahala, ku nace wa yin addu'a.

13. Ku agaji tsarkaka, ku himmantu ga yi wa baƙi alheri.

14. Ku sa wa masu tsananta muku albarka. Ku sa musu albarka, kada ku la'ance su.

15. Ku taya masu farin ciki farin ciki, masu kuka kuwa ku taya su kuka.

16. Ku yi zaman lafiya da juna. Kada ku nuna alfarma, sai dai ku miƙa kanku ga aikata ayyukan tawali'u. Kada ku aza kanku masu hikima ne.

17. Kada ku rama muguntar kowa da mugunta. Ku yi ta lura al'amuranku su zama daidai a gaban kowa.

18. In mai yiwuwa ne, a gare ku, ku yi zaman lafiya da kowa.

19. Ya ku ƙaunatattuna, kada ku ku yi ramuwa, sai dai ku bar wa fushin Allah. Domin a rubuce yake cewa, “Ramuwa tawa ce, ni zan saka, in ji Ubangiji.”

20. Har ma “in maƙiyinka yana jin yunwa, sai ka ci da shi. In yana jin ƙishirwa, ka shayar da shi. Don ta haka ne za ka tula garwashin wuta a kansa.”

21. Kada mugunta ta rinjaye ku, amma ku rinjayi mugunta da nagarta.

Rom 12