Neh 2:11-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Da na iso Urushalima na yi kwana uku,

12. sai na fita da dare tare da waɗansu mutane kima,ban faɗa wa kowa abin da Allahna ya sa a zuciyata in yi wa Urushalima ba. Ba waɗansu dabbobi kuma tare da ni, sai dai dabbar da na hau.

13. Da na fita, sai na bi ta Ƙofar Kwari zuwa Rijiyar Dila da Ƙofar Juji, na dudduba garun Urushalima, wanda aka rushe, da ƙofofinsa da wuta ta cinye.

14. Na yi gaba zuwa Ƙofar Maɓuɓɓuga da Tafkin Sarki, amma dabbar da na hau ba ta sami wurin wucewa ba.

15. Haka kuwa na fita da dare ta hanyar kwari na dudduba garun, sa'an nan na koma ta Ƙofar Kwari.

16. Shugabanni ba su san inda na tafi, ko abin da na yi ba, gama ban riga na faɗa wa Yahudawa, da firistoci, da manyan gari, da shugabanni, da sauran waɗanda za su yi aikin ba.

17. Sa'an nan na ce musu, “Kun ga irin wahalar da muke ciki, yadda Urushalima ta zama kango, an kuma ƙone ƙofofinta. Ku zo, mu sāke gina garun Urushalima don mu fita kunya.”

18. Na kuma faɗa musu yadda Allah yana tare da ni, ya kuma taimake ni, da maganar da sarki ya faɗa mini.Sai suka ce, “Mu tashi, mu kama gini.” Suka himmatu su yi wannan aiki nagari.

Neh 2