Eliyashib, babban firist kuwa, tare da 'yan'uwansa firistoci, suka tashi suka gina Ƙofar Tumaki. Suka tsarkake ta, suka sa mata ƙyamarenta. Suka tsarkake garun zuwa Hasumiyar Ɗari da Hasumiyar Hananel.