Neh 11:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Shugabannin jama'a kuwa suka zauna a Urushalima. Sauran jama'a kuma suka jefa kuri'a don a sami mutum guda daga cikin goma wanda zai zauna a Urushalima, wato tsattsarkan birni, sauran tara kuwa su yi zamansu a sauran garuruwa.

2. Jama'a suka sa wa dukan waɗanda suka tafi su zauna a Urushalima da yardar ransu albarka.

3. Waɗannan su ne shugabannin lardi waɗanda suka zauna a Urushalima, amma a garuruwan Yahuza kowa ya zauna a mahallinsa a garuruwansu, wato Isra'ila, da firistoci, da Lawiyawa, da ma'aikatan Haikali, da zuriyar barorin Sulemanu.

4. Waɗansu mutanen Yahuza da na Biliyaminu suka zauna a Urushalima.Daga cikin mutanen Yahuza akwai Ataya ɗan Azariya, wato jīkan Zakariya ɗan Amariya. Sauran kakanninsa su ne Shefatiya, da Mahalalel, zuriyar Feresa ɗan Yahuza.

5. Akwai kuma Ma'aseya ɗan Baruk, jīkan Kolhoze. Sauran kakanninsa su ne Hazaiya, da Adaya, da Yoyarib, da Zakariya, zuriyar Shela ɗan Yahuza.

6. Dukan mutanen Feresa da suka zauna Urushalima su ɗari huɗu da sittin da takwas ne, dukansu kuwa muhimman mutane ne.

7. Waɗannan su ne mutanen Biliyaminu, Sallai ɗan Meshullam, jīkan Yowed. Sauran kakanninsa su ne Fedaiya, da Kolaiya, da Ma'aseya, da Itiyel da Yeshaya.

8. Sa'an nan kuma ga Gabbai da Sallai danginsa, mutum ɗari tara da ashirin da takwas.

9. Yowel ɗan Zikri shi ne shugabansu, Yahuza ɗan Hassenuwa shi ne shugaba na biyu cikin birnin.

Neh 11