Neh 1:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Labarin Nehemiya ɗan Hakaliya ke nan. Ya zama fa a watan Kisle a shekara ta ashirin, sa'ad da ni Nehemiya nake a fādar Shushan, wato alkarya,

2. sai Hanani, ɗaya daga cikin 'yan'uwana, ya zo tare da waɗansu mutanen Yahuza. Na kuwa tambaye shi labarin Yahudawan da suka tsira, suka koma daga zaman talala, da labarin Urushalima.

3. Sai suka ce mini, “Waɗanda suka tsira, suka koma daga zaman talala, da suke can lardin, suna cikin wahala ƙwarai, suna kuma shan kunya. Garun Urushalima kuma ya rushe, ƙofofi sun ƙone.”

4. Da na ji wannan labari, sai na zauna, na yi kuka. Na yi kwanaki ina baƙin ciki, na yi ta azumi da addu'a a gaban Allah na Sama.

5. Na ce, “Ya Ubangiji Allah na Sama, Allah mai girma, mai banrazana, mai cika alkawari, mai nuna madawwamiyar ƙauna ga waɗanda suke ƙaunarka, wato masu kiyaye umarnanka,

Neh 1