Mika 3:8-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Amma ni ina cike da iko,Da Ruhun Ubangiji,Da shari'a da ƙarfin hali,Don in sanar wa Yakubu da laifinsa,Isra'ila kuma da zunubinsa.

9. Ku ji wannan, ya ku shugabanninjama'ar Yakubu,Da ku sarakunan mutanen Isra'ila,Ku da kuke ƙyamar shari'ar gaskiya,Kuna karkatar da dukan gaskiya.

10. Kuna gina Sihiyona da jini,Kuna kuwa gina Urushalima dazalunci.

11. Shari'ar shugabannin ƙasar ta cinhanci ce.Firistocinta suna koyarwa donneman riba,Haka kuma annabawa suna annabcidon neman kuɗi.Duk da haka suna dogara gaUbangiji, suna cewa,“Ai, Ubangiji yana tsakiyarmu,Ba masifar da za ta same mu.”

12. Saboda ku kuwa za a nome Sihiyonakamar gona,Urushalima kuwa za ta zama tsibinkufai,Dutse inda Haikali yake zai zamakurmi.

Mika 3