Mat 22:10-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Sai bayin suka yi ta bin titi titi, suka tattaro duk waɗanda suka samu, mugaye da nagargaru duka, har wurin bikin ya cika maƙil da baƙi.

11. “Da sarki ya shigo ganin baƙin sai ya ga wani mutum a can wanda bai sa riga irin ta biki ba.

12. Sai ya ce masa, ‘Malam, ta yaya ka shigo nan ba tare da sa riga irin ta biki ba?’ Mutumin kuwa ya rasa ta cewa.

13. Sai sarki ya ce wa barorinsa, ‘Ku ɗaure shi ƙafa da hannu, ku jefa shi cikin matsanancin duhu. Nan za a yi kuka da cizon baƙi.’

14. Gama da yawa ake kira, amma kaɗan ne zaɓaɓɓu.”

15. Sai Farisiyawa suka je suka yi shawara yadda za su burma shi cikin maganarsa.

16. Suka aiko almajiransu wurinsa tare da waɗansu mutanen Hirudus, suka ce, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi, ba ka kuma zaɓen kowa, don ka ɗauki kowa da kowa daidai.

17. To, faɗa mana abin da ka gani. Shin, daidai ne mu biya Kaisar haraji, ko kuwa?”

18. Yesu kuwa domin ya gane muguntarsu, sai ya ce musu, “Don me kuke jarraba ni? Ku munafukai!

19. Ku nuna mini kuɗin harajin.” Sai suka kawo masa dinari.

20. Yesu ya ce musu, “Surar nan da sunan nan na wane ne?”

21. Suka ce, “Na Kaisar ne.” Sa'an nan ya ce musu, “To, sai ku ba Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba Allah abin da yake na Allah.”

22. Da suka ji haka, sai suka yi mamaki, suka rabu da shi, suka yi tafiyarsu.

23. A ran nan sai waɗansu Sadukiyawa (su da suke cewa, ba tashin matattu) suka zo wurinsa, suka yi masa tambaya,

Mat 22