1. Waɗansu Farisiyawa da malaman Attaura suka zo wurin Yesu daga Urushalima, suka ce,
2. “Don me almajiranka suke keta al'adun shugabanni? Domin ba sa wanke hannu kafin su ci abinci.”
3. Sai ya amsa musu ya ce, “Ku kuma don me kuke keta umarnin Allah saboda al'adunku?
4. Domin Allah ya yi umarni ya ce, ‘Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ kuma ‘Wanda ya zagi ubansa ko uwa tasa lalle a kashe shi.’
5. Amma ku kukan ce, ‘Kowa ya ce wa ubansa ko uwa tasa, “Duk abin da dā za ku samu a gare ni an ba Allah,” to, ba lalle ya girmama ubansa ba ke nan.’