Mat 13:35-45 Littafi Mai Tsarki (HAU)

35. Wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Ishaya ne cewa,“Zan yi magana da misalai,Zan sanar da abin da yake ɓoye tun farkon duniya.”

36. Sai ya bar taron, ya shiga gida. Almajiransa kuma suka zo gare shi, suka ce, “Ka fassara mana misalin nan na ciyawa a gonar.”

37. Ya amsa ya ce, “Mai yafa kyakkyawan irin nan, shi ne Ɗan Mutum.

38. Gonar kuwa ita ce duniya, kyakkyawan irin nan, su ne 'ya'yan Mulkin Allah, ciyawar kuwa, 'ya'yan Mugun ne.

39. Magabcin nan da ya yafa ta kuwa, Iblis ne. Lokacin yankan kuwa, ƙarshen duniya ne, masu yankan kuma, mala'iku ne.

40. Kamar yadda ake tara ciyawa a ƙone ta, haka zai kasance a ƙarshen duniya.

41. Ɗan Mutum zai aiko mala'ikunsa, za su tattaro duk masu sa mutane laifi, da kuma duk masu yin mugun aiki, su fitar da su daga Mulkinsa,

42. su kuma jefa su cikin wuta mai ruruwa. Nan za su yi kuka da cizon haƙora.

43. Sa'an nan ne masu adalci za su haskaka kamar rana a Mulkin Ubansu. Duk mai kunnen ji, yă ji.”

44. “Mulkin Sama kamar dukiya yake da take binne a gona, wadda wani ya samu, ya sāke binnewa. Yana tsaka da murna tasa, sai ya je ya sayar da dukan mallaka tasa, ya sayi gonar.”

45. “Har wa yau kuma Mulkin Sama kamar attajiri yake, mai neman lu'ulu'u masu daraja.

Mat 13