2. Dukan wuraren zaman Yakubu,Ubangiji ya hallakar ba tausayi,Da fushinsa kuma ya rurrushe kagaran Sihiyona.Ya ƙasƙantar da mulki da masu mulkin.
3. Da zafin fushinsa, ya karya ƙarfin Isra'ila,Ya kuma bar yi musu taimakoA lokacin da abokan gāba suka zo.Kamar harshen wuta, ya ƙone dukan abin da yake na Yakubu.
4. Ya ja bakansa kamar abokan gāba,Ya kuma nuna ikonsa kamar maƙiyi.Ya hallaka dukan abin da yake da bansha'awa.A alfarwar Sihiyona, ya zubo da hasalarsa kamar wuta.
5. Ubangiji ya zama kamar maƙiyi, ya hallaka Isra'ila.Ya hallaka fādodinta duka,Ya mai da kagaranta kango.Ya aukar wa Yahuza da makoki da baƙin ciki mai yawa.
6. Ya rushe Haikalinsa kamar bukka cikin gona,Ya mai da wurin yin ƙayyadaddun idodinsa kufai.Ubangiji ya sa ƙayyadadden idi da kiyaye AsabarSu ƙare a Sihiyona,Da zafin fushinsa kuma ya wofinta sarki da firist.