17. Ubangiji ya aikata abin da ya yi niyya,Ya cika maganarsa wadda ya faɗa tun dā,Ya hallakar, ba tausayi,Ya sa maƙiyi ya yi murna a kanki,Ya ƙarfafa ƙarfin maƙiyanki.
18. Ya Sihiyona, ki yi kuka ga Ubangiji,Bari hawayenki su gudana dare da rana kamar ruwan rafi,Kada ki huta, kada kuma idanunki su huta!
19. Ki tashi, ki ya ta kuka dukan dare,Ki bulbule abin da yake cikin zuciyarkiKamar ruwa gaban Ubangiji.Ki miƙa hannuwanki zuwa gare shi,Saboda rayukan 'ya'yanki,Waɗanda suke suma da yunwaA magamin kowane titi!
20. Ya Ubangiji, ka duba, ka gani!Wane ne ka yi wa haka?Mata za su cinye 'ya'yansu da suke reno?Ko kuwa za a kashe firist da annabiA cikin Haikalin Ubangiji?
21. Yara da tsofaffi suna kwance cikin ƙurar tituna,An kashe 'ya'yana, 'yan mata da samari, da takobi.Ka kashe su a ranar fushinka, ba tausayi.
22. Ka gayyato mini tsoroKamar yadda akan gayyato taro a ranar idi.A ranar fushin UbangijiBa wanda ya tsere, ko wanda ya tsira.'Ya'yan da na yi renonsu, na goye su,Maƙiyina ya hallaka su.