Mak 2:10-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Dattawan Sihiyona suna zaune a ƙasa shiru,Sun yi hurwa, suna saye da tufafin makoki.'Yan matan Urushalima kuma sun sunkuyar da kansu ƙasa.

11. Idanuna sun dushe saboda kuka,Raina yana cikin damuwa.Zuciyata ta karai saboda halakar mutanena,Gama 'yan yara da masu shan mamaSun suma a titunan birnin.

12. Suna yi wa uwayensu kuka, suna cewa,“Ina abinci da ruwan inabi?”Suna suma kamar mutanen da aka yi wa rauniA titunan birnin,Suna mutuwa a ƙirjin uwayensu.

13. Me zan ce miki?Da me zan kwatanta ki, ya Urushalima?Da me zan misalta wahalarkiDon in ta'azantar da ke, ya Sihiyona?Masifar da ta same ki tana da fāɗi kamar teku,Wa zai iya warkar da ke?

Mak 2