Mak 1:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Urushalima wadda take cike da mutane a dā,Yanzu tana zaman kaɗaici!Tana zama kamar mace wadda mijinta ya rasu,Ita wadda dā ta zama babba a cikin sauran al'ummai!Ita wadda take a dā sarauniya a cikin larduna,Ta zama mai biyan gandu!

2. Da dare tana kuka mai zafi,Hawaye suna zuba sharaf-sharaf a kumatunta.Dukan masoyanta ba wanda yake ta'azantar da ita.Dukan abokanta sun ci amanarta, sun zama maƙiyanta.

3. Yahuza ta tafi bauta tana shan azaba,Da bauta mai tsanani.Tana zaune a tsakiyar sauran al'umma,Amma ba ta sami hutawa ba,Gama masu runtumarta sun ci mata, ba hanyar tsira.

Mak 1