6. Ba ku ci hatsi ba, ba ku kuma sha ruwan inabi ba, ko barasa, don ku sani shi ne Ubangiji Allahnku.
7. Sa'ad da kuka isa wannan wuri, sai Sihon Sarkin Heshbon, da Og, Sarkin Bashan, suka fito su yi yaƙi da mu, amma muka ci su.
8. Muku ƙwace ƙasarsu, muka ba Ra'ubainawa, da Gadawa, da rabin kabilar Manassa, su gāda.
9. Saboda haka sai ku kiyaye, ku aikata dukan zantuttukan wannan alkawari don ku arzuta a cikin dukan abin da za ku yi.
10. “Yau, ga ku nan tsaye, dukanku a gaban Ubangiji Allahnku, shugabannin kabilanku, da dattawanku, da shugabannin sojojinku, da dukan mazajen Isra'ila,
11. da 'ya'yanku, da matanku, da baƙin da suke a zangonku, da mai yi muku faskare ko mai ɗebo muku ruwa.
12. Don ku ƙulla alkawari da Ubangiji Allahnku, alkawarin da Ubangiji Allahnku yake yi da ku yau.
13. Don ya mai da ku jama'arsa yau, shi kuma ya zama Allahnku kamar yadda ya yi muku magana, da yadda kuma ya rantse wa kakanninku, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.
14. Ba da ku kaɗai nake yin wannan alkawari ba,
15. amma da wanda ba ya nan tare da mu yau, da shi wanda yake tare da mu a nan yau, a gaban Ubangiji Allahnmu.
16. “Kun sani dai yadda muka zauna a ƙasar Masar, da yadda muka yi ta ratsawa ta tsakiyar al'ummai muka wuce.
17. Kun ga abubuwan da suke da su masu banƙyama, wato gumakansu na itace, da na dutse, da na azurfa, da na zinariya.
18. Kada zuciyar wani mutum, ko ta wata mata ko na wani iyali, ko wata kabila cikinku yau, ta bar bin Ubangiji Allahnku, ta koma ga bauta wa gumakan al'umman nan. Kada a iske wani tushe a cikinku mai ba da 'ya'ya masu dafi, masu ɗaci.
19. Idan wani mutum ya ji zantuttukan la'anan nan sa'an nan ya sa wa kansa albarka a zuciyarsa, yana cewa, ‘Ba abin da zai same ni ko na bi taurin zuciyata,’ wannan zai haddasa lalacewar ɗanye da busasshe gaba ɗaya.
20. Ubangiji ba zai gafarce shi ba, amma fushin Ubangiji da kishinsa za su auko a kan wannan mutum, dukan la'anar kuma da aka rubuta a littafin nan za ta bi ta kansa, Ubangiji kuma zai shafe sunansa daga duniya.
21. Ubangiji zai ware mutumin nan daga dukan kabilan Isra'ila, don ya hukunta shi bisa ga dukan la'anar da aka rubuta a wannan littafin dokoki.