44. Za ku karɓi rance a wurinsu, su ba za su karɓi rance a wurinku ba. Su za su zama kai, ku kuwa za ku zama wutsiya.
45. “Dukan waɗannan la'anoni za su auko muku, su bi ku, su same ku, har ku hallaka, domin ba ku yi biyayya da Ubangiji Allahnku ba, ba ku kiyaye umarnai da dokoki da ya umarce ku da su ba.
46. Za su zama alama da abin mamaki a kanku da zuriyarku har abada.
47. Ba ku bauta wa Ubangiji Allahnku da murna da farin ciki ba, saboda dukan abin da ya ba ku a yalwace,
48. domin haka za ku bauta wa magabtanku waɗanda Ubangiji zai turo muku. Za ku bauta musu da yunwa, da ƙishirwa, da tsiraici, da talauci. Za su sa karkiyar ƙarfe a wuyanka har su hallaka ku.
49. Ubangiji zai kawo wata al'umma daga nesa, wato daga bangon duniya, mai kai sura kamar gaggafa, wadda za ta yi gāba da ku. Al'ummar da ba ku san harshenta ba,
50. al'umma mai zafin hali, wadda ba ta kula da tsofaffi, ba ta kuma jin tausayin yara.
51. Za ta ci shanunku da amfanin ƙasarku har ku hallaka. Ba za ta bar muku hatsi ko ruwan inabi, ko mai, ko 'ya'yan shanunku, ko na tumaki da na awakinku ba, har ta lalatar da ku.
52. Za su kewaye garuruwanku da yaƙi, har dogayen garukanku, da kagaranku waɗanda kuke dogara gare su, su rurrushe. Za su kewaye garuruwan ƙasarku da yaƙi a ƙasar da Ubangiji Allahnku ya ba ku.
53. Za ku ci naman 'ya'yanku, mata da maza, waɗanda Ubangiji Allahnku ya ba ku, saboda irin tsananin kewayewar da magabtanku suka yi muku da yaƙi.
54. Nagarin mutum mai taushin zuciya wanda yake tare da ku, zai ƙi ɗan'uwansa, da matarsa, da 'ya'yansa da suka ragu,