M. Sh 28:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, kuna aikata dukan umarnansa waɗanda nake umartarku da su yau, to, Ubangiji Allahnku zai fifita ku fiye da dukan sauran al'umma.

2. Idan kun yi biyayya da maganar Ubangiji Allahnku, dukan albarkun nan za su sauko muku, su zama naku.

3. “Za ku zama masu albarka, ko kuna cikin gari, ko kuna cikin karkara.

4. “'Ya'yanku za su zama masu albarka, haka nan kuma amfanin gonakinku, da 'ya'yan dabbobinku, da 'ya'yan shanunku, da 'ya'yan tumakinku da awakinku.

5. “Kwandunanku da makwaɓan za su yalwata ƙullunku.

6. “Da albarka za ku shiga, da albarka kuma za ku fita.

7. “Ubangiji zai sa ku fatattaki abokan gābanku a gabanku waɗanda suke tasar muku. Ta hanya guda za su auka muku, amma ta hanyoyi bakwai za su gudu daga gabanku.

8. “Ubangiji zai sa wa abin da yake cikin rumbunanku albarka da dukan aikin hannuwanku. Zai sa muku albarka a ƙasar da yake ba ku.

9. “Ubangiji zai sa ku zama tsattsarkar jama'arsa kamar yadda ya rantse muku, idan za ku kiyaye umarnan Ubangiji Allahnku, ku yi tafiya cikin tafarkunsa.

10. Dukan mutanen duniya za su gane ku na Ubangiji ne, za su ji tsoronku.

11. Ubangiji zai arzuta ku ƙwarai da 'ya'ya, da 'ya'yan dabbobi, da amfanin gona, a ƙasar da Ubangiji ya rantse wa kakanninku zai ba ku.

12. Ubangiji zai buɗe muku taskarsa ta sammai, don ya ba ƙasarku ruwa a kan kari, zai kuma sa albarka a kan dukan aikin hannuwanku. Al'ummai da yawa za su karɓi rance a wurinku, amma ku, ba za ku karɓi rance ba.

M. Sh 28