12. Amma kada ku yarda abin da aka jinginar ya kwana a wurinku idan mutumin matalauci ne.
13. Sai ku mayar masa da shi a faɗuwar rana domin ya yi barci yafe da rigarsa ya gode muku. Yin haka zai zama muku adalci a wurin Ubangiji Allahnku.
14. “Kada ku zalunci ɗan ƙodago wanda yake matalauci, ko shi danginku ne, ko kuwa baƙon da yake zaune a garuruwan ƙasarku.
15. Sai ku biya shi hakkinsa a ranar da ya yi aikin, kafin faɗuwar rana, gama shi matalauci ne, zuciyarsa tana kan abin hakkinsa, don kada ya yi wa Ubangiji kuka a kanku, har ya zama laifi a gare ku.
16. “Kada a kashe ubanni maimakon 'ya'ya, kada kuma a kashe 'ya'ya maimakon ubanni. Amma za a kashe mutum saboda laifin da ya aikata.
17. “Kada ku karkatar da shari'ar baƙo ko maraya. Kada kuma ku karɓi mayafin matar da mijinta ya rasu abin jingina.
18. Ku tuna, dā ku bayi ne a Masar, Ubangiji Allahnku ya fanshe ku daga can, saboda haka ina umartarku ku yi wannan.
19. “Idan kun manta da wani dami a gona lokacin girbin amfanin gona, kada ku koma ku ɗauko. Ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske, domin Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka a kan dukan aikin hannuwanku.
20. Sa'ad da kuka kakkaɓe 'ya'yan zaitunku, kada ku sāke bin rassan kuna kakkaɓewa, sai ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske.
21. Sa'ad da kuka girbe gonar inabinku kada kuma ku yi kala, sai ku bar wa baƙo, da maraya, da gwauruwa ta gaske.
22. Sai ku tuna, dā ku bayi ne a Masar, don haka nake umartarku ku yi wannan.”