1. “A ƙarshen kowace shekara bakwai dole ku yafe dukan basusuwan da kuke bi.
2. Ga yadda za ku yafe. Sai kowane mai bin bashi ya yafe wa maƙwabcinsa, kada ya karɓi kome a hannun maƙwabcinsa ko ɗan'uwansa, gama an yi shelar yafewa ta Ubangiji.
3. Kana iya matsa wa baƙo ya biya ka, amma sai ka yafe wa danginka bashin da kake binsa.
4. “Ba za a sami matalauci a cikinku ba, da yake Ubangiji Allahnku zai sa muku albarka a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ita gādo, ku mallaka,
5. muddin kun yi biyayya da muryar Ubangiji Allahnku, kuna kiyaye wannan umarni da na umarce ku da shi yau.
6. Ubangiji Allahnku zai sa muku albarka kamar yadda ya alkawarta. Za ku ba al'ummai da yawa rance, amma ba za ku bukaci rance don kanku ba. Za ku mallaki al'ummai da yawa, amma su ba za su mallake ku ba.
7. “Idan akwai wani danginku matalauci, a wani gari na cikin garuruwan ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku, to, kada ku taurara zuciyarku, ku ƙi sakin hannu ga danginku matalauci.
8. Amma ku ba shi hannu sake, ku ranta masa abin da yake so gwargwadon bukatarsa.
9. Amma fa, ku lura, kada ku yi tunanin banza a zuciyarku, kuna cewa, ‘Ai, shekara ta bakwai, shekarar yafewa ta yi kusa,’ har ku ɗaure wa danginku matalauci fuska, ku ƙi ba shi kome. Zai yi kuka ga Ubangiji a kanku, abin kuwa zai zama laifi a kanku.
10. Sai ku ba shi hannu sake, ba da ɓacin zuciya ba. Saboda wannan Ubangiji zai sa muku albarka cikin aikinku duka, da abin da kuke niyyar yi.
11. Gama ba za a rasa matalauta a ƙasar ba, saboda haka nake umartarku, cewa ku zama da hannu sake ga 'yan'uwanku, da mabukaci, da matalauci.”
12. “Idan aka sayar muku da Ba'ibrane ko mace ko namiji, to, sai ya bauta muku shekara shida, amma a ta bakwai, sai ku 'yantar da shi.
13. Idan kuma kun 'yantar da shi, kada ku bar shi ya tafi hannu wofi.